Yanzu-yanzu: Tinubu ya sauke ministoci biyu

Bola Tinubu Tinubu aaaaaaaaaaa 700x430

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da sake fasalin majalisar zartarwa, inda ya cire ministan kudi hadin gwiwa da tattalin, Wale Edun da ministan gidaje da raya birane, Ahmed Dangiwa daga majalisar.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin mataimaki na musamman ga sakataren gwamnatin tarayya kan kafafen watsa labarai, Yomi Odunuga, inda ya bayyana hakan na cikin wani sako da sakataren gwamnatin tarayya George Akume ya sanyawa hannu a ranar Talata.

Sanarwar ta kuma ce, an nada Taiwo Oyedele a matsayin sabon ministan kudi da hadin gwiwar tattalin arziki, yayin da aka kuma nada Dr Muttaqha Darma a matsayin ministan gidaje da raya birane.

Haka zalika, sanarwar ta bukaci ministocin da aka sauke da su mika ragamar ma’aikatun ga magadansu ko kuma masu sanya idanu a ma’aikatun. “Dole ne mika ragamar da fara aikin sabbin ministocin ta fara nan da ranar Alhamis 23 ga watan Afrilun da muke ciki.

Akume, ya kuma kara da cewa an yi sauye-sauyen domin ingantawa tare da karawa duk bangarorin gwamnati karfi, musamman a bangaren tattalin arziki a karkashin kudurin gwamnati na Renewed Hope Agenda.

Inda yace shugaban kasa ya yi hakan ne bisa damar da kundin tsarin mulkin kas ana 1999 da aka yi wa gara, sashi na 147 dana 148 ya bashi.
Sakataren ya kuma cewa shugaban kasar ya nuna jindadin shi tare da gode wa ministocin bisa aikin hidimta wa kasa da suka yi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here