Hukumar kula da jin daɗin mahajjata ta jihar Kano ta sanar a ranar Litinin cewa ta rufe karɓar kuɗin rajista na aikin Hajjin shekarar 2026, bisa jadawalin da ta tsara na haɗa bayanai game da wa dansa za su amfani da damar kafin ƙarewar lokaci.
Daraktan hukumar, Laminu Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗar jama’a na hukumar Sulaiman Dederi ya fitar a Kano, yana mai cewa ranar jumma’a ce ta kasance ƙarshe ga duk masu niyyar biyan kuɗin.
Sanarwar ta fayyace cewa hukumar ba za ta tsawaita wa’adin ba, domin bayanin da aka samu a taron da aka gudanar tare da hukumar kula da aikin Hajji ta ƙasa NAHCON a abuja ya tabbatar da cewa babu damar tsawaitawa.
Taron ya tabbatar da cewa rufe karɓar kuɗin da wuri ya zama dole saboda wasu sabbin ƙa’idoji da hukumomin Saudiya suka gabatar, waɗanda suka wajabta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji tun da wuri tare da bin matakai yadda ya kamata.
Daraktan ya tabbatar da cewa hukumar tana ci gaba da himma wajen samar da ingantattun ayyuka ga duk masu niyyar zuwa aikin hajji, tare da tabbatar da cewa duk matakan gudanarwa sun bi ka’idojin ƙasa da ƙasa.
Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar za ta tabbatar da cika ƙa’idodi gaba ɗaya domin sauƙaƙa shirye-shirye da tafiyar da aikin Hajjin shekarar 2026, kamar yadda ake buƙata.












































