YANZU-YANZU Bama-bamai sun tashi a Maiduguri gabanin ziyarar Shugaba Buhari

F6E78565 984F 42C8 9BC6 1AB23E59BA95
F6E78565 984F 42C8 9BC6 1AB23E59BA95

Kimanin mutane hudu ne suka mutu ranar Alhamis bayan wasu bama-bamai uku suka tashi a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Fashe-fashen na zuwa ne yayin da ya rage ‘yan sa’o’i kadan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara a jihar, inda lamarin ya yi sanadin jikkata mutane kusan takwas.

Solacebase ta tattaro cewa lamarin ya afku nw a wurare uku – Bulumkutu, Cross Ajilari da kuma Ayaje.

Majiyoyi sun ce an samu asarar rayuka a Ayaje da Bulumkutu, sai dai kawo yanzu babu wani bayani daga Ajilari.

Shugaba Buhari zai kaddamar da wani katafaren gini da Mohammed Indimi ya bayar ga jami’ar Maiduguri.

Ana kuma sa ran zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar Borno ta aiwatar.

Cikakkun bayanai suna nan tafe

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here