Tsoffin daliban Sashen Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Bayero da ke Kano aji na 1998, sun karrama Malamansu 10, wadanda suka koyar da su a lokacin da suna jami’a har suka zama abin da suke a yau.
Wadanda aka karrama sun hada da Shugaban Sashen na yanzu Farfesa Abdulmalik Auwal da Farfesa Habu Muhammad Daraktan cibiyar nazarin dimokuradiyya ta Jami’ar Bayero, wato Mubayya House.
Sauran sun hada da Farfesa Attahiru Jega da Farfesa Mahmud Lawan da Farfesa Abubakar Jika Jiddere sai Dakta Ibrahim Mu’azzam da Farfesa Aisha Isma’il da Malam Mu’azu Yusif da kuma Malam Salisu Yusuf.

A nasa jawabin jagoran tsaffin daliban Alhaji Kabiru Nuhu Dan Liman ya yi godiya ga Allah madaukakin sarki bisa daukakar da suka samu a fannonin ayyuka daban-daban.
Ya ce sun shirya taron ne domin ganawa da juna, da yi wa abokan karatunsu da suka rasu addu’a tare da tallafa wa Iyalansu.
Karanta wannan: FASSARAR JAWABIN SHUGABAN KASA BOLA AHMED TINUBU A SABUWAR SHEKARAR 2024
Ya kara da cewa taron ya tuna musu abubuwan da yawa a lokacin suna karatu a jami’a shekaru 25 da suka gabata.
Da yake jawabi tun farko, Farfesa Mahmud Lawan, guda cikin malamansu a wancan lokaci ya taya tsofaffin daliban murnar sake haduwa da juna bayan shekaru 25 da kammala jami’a.
“Ina so in taya ku murna la’akhari da yadda kuka hada kan ku a wannan waje, ina farin cikin ganin ku a yau, kuna daga cikin jerin dalibai nagari, abin da ku ka yi babban abin tarihi ne da za a yaba”. Inji shi.
Karanta wannan: Zan rike amanar da ‘Yan Nijeriya suka bani-Tinubu
A nasa bangaren, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya bayyana jin dadinsa, inda ya ce ba zai iya kwatanta farin cikinsa ba, tare da bayyana ranar a matsayin ranar da ba za su taba mantawa da ita ba.
Ya ce ko shakka babu taron ya kara musu kwarin guiwa a matsayinsu na malamai, kuma za su ci gaba da yin iya kokarinsu wajen ganin sun ci gaba da yaye dalibai nagari.
Yayin taron an yi wasanni na abokai kamar yadda aka saba, kuma ‘yan ajin sun halacci taron daga ko ina a fadin kasar nan.













































