Wasu ƴan bindiga sun kashe babban basaraken garin Orsu Obodo da ke karamar hukumar Oguta a jihar Imo, Eze Victor Ijioma da kuma wazirin garin Mgbele shi ma a karamar hukumar.
Rahotanni sun ce maharan sun kashe shugabannin gargajiyar ne a hare daban-daban a jiya Alhamis.
Ƴan bindigar da ba a san ko su wanene ba zuwa yanzu sun hallaka babban basaraken ne a motarsa a garin Izombo kuma suka banka masa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani da ya ga yadda abin ya faru wanda bai yarda a bayyana sunansa ba ya ce maharan sun tare basaraken na al’ummar Orsu Obodo a mahadar Umuamaka a garin Izombe da ke makwabtaka da nasu, inda suka hallaka shi.
Ya kara da cewa domin su tabbatar da ya mutu ne suka sanya wa gawarsa a cikin motar wuta.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa kakakin rundunar ƴan sanda a jihar Henry Okoye ya tabbatar mata da labarin kashe-kashen yau Juma’a.
Kuma ya ce Kwamishina ƴan sandan jihar Muhammed Barde ya kaddamar da binciken zakulo maharan.
Kashe-kashe da ƴan bindiga kan yi a jihar ta Imo sun karu tun bayan zabun da aka yi na jihar da kuma na tarayya.













































