https://solacebasehausa.com/wp-content/uploads/2023/04/Glano-750×430-4.jpeg”><i.
Hukumar kula da kadarorin Najeriya (AMCON) ta ce ta kwace kadarori na kamfanin Glano Nigeria Limited kan bashin da yake bin kamfanin da ya kai Naira biliyan 2.4.
A cikin wata sanarwa da shugaban sashjn sanarwa na kamfanin Jude Nwauzor, ya ce kwacen ya biyo bayan umarnin wata babbar kotun tarayya da ke Legas.
Saboda haka, ya ce kamfanin ya mallaki kadarorin kamfanin, dake Fatakwal, jihar Rivers, a ranar 6 ga Afrilu, 2023.
Sanarwar ta ce, AMCON, wadda aka kafa domin karbo bashi a madadin gwamnatin tarayya, ta kasance cikin sharia a kotu da Glano da masu tallata shi tun 2016 amma ta yi hakuri har zuwa 2018”.
Ta ce daga karshe kotu ta yanke shawarar marawa AMCON kwace Glano, bayan ta duba lamarin gaba dayansa – musamman dangane da kokarin da AMCON ta yi na bi cikin ruwan sanyi dan kwace kadarorin".
“A bisa bin umarnin tilastawa, AMCON a ranar Alhamis, 6 ga Afrilu, 2023, ta kwace kadarorin Glano Nigeria Limited da ke a no. 22 Woji road Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers, wanda ke karkashin kulawar Sterling Law Alliance tun 2019, "inji shi.
Ya kara da cewa an aiwatar da aikin ne cikin “hankali” musamman yadda kotun ta kuma umurci rundunar ‘yan sandan Najeriya da jami’an kotun da sauran jami’an tsaro da su taimaka wa kamfanin wajen kwato kadarorin.










































