Ƴan sanda za su ci gaba da aiwatar da dokar lasisin baƙin gilashin mota

tinted permit 716x430

Rundunar ‘yan sanda ta ƙasa ta bayyana cewa za ta ci gaba da aiwatar da dokar lasisin baƙin gilashin mota, bayan ta kammala nazari kan matsalolin tsaro da ke ƙaruwa da kuma bukatar kare lafiyar al’umma a faɗin ƙasa.

Rundunar ta bayyana cewa batun yana gaban kotu, amma babu wani umarni daga kotu da ya hana ‘yan sanda aiwatar da dokokin da suka shafi hana amfani da gilashin mota mai duhu, don haka rundunar ke da ikon ci gaba da aiki da dokar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ƙasa, CSP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa rundunar ta taɓa dakatar da aiwatar da dokar ne domin bai wa masu ababen hawa damar daidaita takardunsu da kammala rajista ba tare da matsin lamba ba.

Ya ce sabon bincike ya nuna karuwar ayyukan ta’addanci da manyan laifuka da ake aikatawa ta hanyar amfani da motocin da suke da baƙin gilashi, ba tare da izini ba, lamarin da ke bai wa masu laifi damar ɓoye fuska da kauce wa ganowa.

Rundunar ta jaddada cewa wasu mutane da ƙungiyoyin masu aikata laifuka suna amfani da wannan gibi wajen aikata fashi da makami, sace-sace da kuma sauran munanan laifuka, wanda hakan ke zama barazana ga tsaro da zaman lafiyar jama’a.

A sakamakon haka, rundunar ‘yan sandan ƙasa ta bayyana cewa dole ne ta dawo da cikakken aiwatar da dokar cikin gaggawa, tare da tabbatar da mutunta haƙƙin ‘yan ƙasa da bin dukkan dokoki da ƙa’idojin da suka dace.

Sufeto Janar na ‘yan sanda Kayode Egbetokun ya tabbatar da aniyar rundunar na kare lafiyar jama’a da aiki tare da masu ruwa da tsaki, yayin da aka ƙarfafa masu bukatar lasisin baƙin gilashin mota su bi hanyoyin da aka amince da su kamar yadda doka ta tanada.

NAN.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here