Kungiyar Gwamnoni ta Progressives Governors Forum (PGF) ta yi watsi da ikirarin cewa jam’iyyar APC na jan ragamar Najeriya zuwa jam’iyya daya.
Ƙungiyar ta bayyana irin waɗannan zarge-zargen a matsayin marasa tushe, tana mai cewa suna nuna karɓuwar da jam’iyya mai mulki ke samu a tsakanin ’yan ƙasa.
Shugaban ƙungiyar, gwamnan jihar Imo Hope Uzodimma, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai bayan taron gwamnonin APC da aka gudanar a birnin Abuja.
Ya ce ƙaruwa da tasirin APC ya samo asali ne daga gamsuwar jama’a da ayyukan jam’iyyar, ba wai yunƙurin danne adawa ba.
Labari mai alaƙa: Gambari ya nuna damuwa kan yiwuwar Najeriya na karkata zuwa tsarin jam’iyya ɗaya
Uzodimma ya bayyana cewa yawaitar gwamnonin da ke shiga APC alama ce ta yadda ayyukan shugaban ƙasa ke samun karɓuwa, tare da nuna cewa jam’iyyar na tafiya kan turba mai kyau wajen samar da walwala ga ’yan Najeriya.
Ya ƙara da cewa wannan karɓuwa na nuna goyon bayan ’yan siyasa da sauran ’yan ƙasa masu niyyar ci gaban ƙasa.
Ya yi kira ga ’yan siyasa da al’ummar ƙasa da su bai wa zaman lafiya dama, yana mai cewa haɗin kai ne zai kai Najeriya ga girma da ɗaukaka.
A cewarsa, haɗin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban ne zai tabbatar da dorewar ci gaba.
Uzodimma ya kuma nuna cewa shigar sabbin mambobi cikin APC, ciki har da gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, alama ce ta amincewar jama’a da jam’iyyar.
Ya ce yawan gwamnonin APC ya haura 28, wanda ke nuna ƙarfinta a fagen siyasar ƙasa da goyon bayan da take samu ga manufofin shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin na aiwatar da sauye-sauyen da ke da tasiri mai kyau, ciki har da tsarin rancen ɗalibai da aka kafa domin tabbatar da cewa babu ɗan Najeriya da za a hana ilimi saboda rashin kuɗi, da kuma faɗaɗa tsarin inshorar lafiya domin sauƙaƙa samun kulawar lafiya.
Uzodimma ya ƙara da cewa ingantuwar tattalin arziƙi, ƙaruwa da kuɗaɗen shiga na gwamnati, da haɓakar samarwa a ɓangaren man fetur da gas na nuna cewa ƙasar na kan hanyar farfaɗowa.
Ya buƙaci ’yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa masu fata da yaba da ci gaban da ake samu a ƙarƙashin wannan gwamnati.
NAN













































