‘Ƴan sanda sun tabbatar da mutuwar ƙarin mutum 3 a jihar Bauchi

'yar sanda, mutuwar, jihar, bauchi
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar ƙarin mutum uku sakamakon turmutsitsin da aka yi a jihar Bauchi lokacin raba zakkar kuɗi.Tun da farko...

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar ƙarin mutum uku sakamakon turmutsitsin da aka yi a jihar Bauchi lokacin raba zakkar kuɗi.

Tun da farko hukumomi sun tabbatar da mutuwar mata huɗu.

Sai dai wani ɗan jarida a jihar ta Bauchi Hassan Mohammed wanda ke bibiyar lamarin, ya ce yana tunanin mutanen da suka mutu za su kai kusan 17.

Karin labari: Mutum 3 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Nairobi

Ƴan sanda sun ce sun ƙaddamar da bincike game da turmutsitsin da ya janyo mutuwar mutanen.

Najeriya dai ta shafe watanni tana fama da matsin tattalin arziki har da tashin farashin kayayyaki.

A ranar Juma’a, an samu ɗaliban jami’ar jihar Nasarawa da suka mutu a irin wannan turmutsitsin na raba abinci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here