Zan iya shiga APC nan ba da jimawa ba – Janar Musa

Christopher Musa 750x430

Ministan tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya nuna yiwuwar shigarsa jam’iyyar APC nan gaba, inda ya bayyana cewa a halin yanzu yana cikin wani yanayi na sauyin matsaya a harkar siyasa.

Janar Musa, wanda ya taɓa rike muƙamin Babban Hafsan Tsaro na ƙasa, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin siyasa na tashar talabijin na Channels da ake gabatarwa a ranakun Lahadi.

Da aka tambaye shi ko yana kallon kansa a matsayin ɗan siyasa a yanzu, ya bayyana cewa har yanzu bai kammala sauya matsayarsa ba, sai dai yana cikin matakin sauyin siyasa.

Game da shigarsa jam’iyyar APC mai mulki, Ministan tsaron ya bayyana cewa har yanzu bai shiga jam’iyyar ba, amma yana ganin hakan na iya faruwa, kasancewar jam’iyyar ta ba shi dama da kafar da ya bayyana kansa tun daga lokacin da yake Babban Hafsan Tsaro zuwa yanzu.

Tsohon Babban Hafsan Tsaron, Janar Christopher Musa, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya rantsar da shi a matsayin Ministan Tsaro a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Villa, bayan ritayarsa daga aikin soja.

Ministan ya kuma bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya cancanci cikakken goyon baya, inda ya jaddada shirinsa na mara wa gwamnatinsa baya ta kowace hanya, ciki har da taimakawa domin samun nasarar kammala wa’adi na biyu idan lokaci ya yi.

Kalaman Ministan sun zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun sauya sheƙa zuwa APC tun bayan hawan Shugaba Tinubu mulki, inda gwamnonin jihohi da dama daga jam’iyyun adawa, ciki har da gwamnan Kano Abba Yusuf na NNPP da wasu daga PDP, suka koma jam’iyyar mai mulki, lamarin da ke ƙara tayar da muhawara kan yanayin siyasar ƙasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here