Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro a faɗin ƙasar, tare da bayar da umarnin ɗaukar karin jami’an ’yansanda da na rundunar sojoji domin magance karuwar matsalolin tsaro.
Sanarwar da aka fitar daga fadar shugaban ƙasa ta nuna cewa shugaban ya umurci rundunar ’yansanda da ta ɗauki karin jami’ai 20,000, wanda ya kai jimillar wadanda za a ɗauka zuwa 50,000.
Ya kuma amince a yi amfani da sansanonin NYSC a matsayin cibiyoyin horar da sabbin jami’an.
Sanarwar ta bayyana cewa wannan mataki ya haɗa da umarnin cewa jami’an da za a janye daga ayyukan tsaron mutane na musamman su sami horo na gaggawa domin su koma yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
Shugaban ya bai wa hukumar DSS umarnin tura dakarun tsaron dazuka domin damke ’yan ta’adda da ’yan fashi da ke buya a dazuka, tare da taƙaita musu wuraren ɓoye.
Tinubu ya ce wannan lokaci na bukatar haɗin kai, yana mai kira ga ’yan Najeriya su shiga tsakani wajen taimakawa hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a yankuna masu fama da hare-hare.
Shugaban ya yaba wa hukumomin tsaro bisa ceto dalibai 24 a Kebbi da masu ibada 38 a Kwara, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da aiki tukuru wajen kubutar da daliban da ke hannun masu garkuwa a Jihar Neja.
Ya kuma nuna cewa ya dace majalisar dokoki ta duba yiwuwar kafa rundunar ’yansanda ta jihohi, tare da kira ga hukumomin ƙananan hukumomi da na addinai su ƙara tsaurara tsaro a wuraren taro.
Shugaban ya jaddada bukatar kiyayewa daga kiwo a fili, yana mai kira ga makiyaya su rungumi kiwon zamani ta hanyar ruga tare da mika miyagun makamai.
Ya ce kafa Ma’aikatar Livestock na daga cikin matakan magance rikicin manoma da makiyaya gaba ɗaya.
Ya ƙara da cewa jama’a su guji firgita, su ci gaba da bayar da rahoton duk wani abu da ke haifar da zargi tare da tallafa wa jami’an tsaro domin tabbatar da samun dawwamammen zaman lafiya a ƙasar.













































