Jam’iyyar PDP a yankin Kudu maso Yammacin kasar nan ta bukaci shugaban jam’iyyar PDP na kasa Sanata Iyorchia Ayu da ya yi murabus.
A wani taro da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Alhaji Atiku Abubakar yayi da gwamna Makinde a badin.
Gwamnan Oyo tare da Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike sun jima suna takun-saka da Jam’iyyar PDP kan Shugaban Jam’iyyar na kasa da kuma dan takarar Shugaban kasa wadanda dukkan su suka fito daga yankin Arewa.
Makinde ya ce, “Shekaru takwas da APC ta yi ta yi mana surutai. Matsalar ita ce dole ne mu yi abin da muke tunasar wa. Idan har muna son hada kan Najeriya, dole ne mu hada kan PDP tukunna.
“Sakon da PDP ta Kudu maso Yammacin kasar nan na neman a sake fasalin kwamitin gudanarwar jamiyar baki daya”.













































