YANZU YANZU: Kotu ta umarci Sojoji da su biya Nnamdi Kanu naira biliyan 1, sannan su nemi afuwar

Wata babbar kotun jihar Abia ta umurci gwamnatin tarayya da sojojin Najeriya da su biya shugaban masu fafutukar kafa kasar Biyafara Mazi Nnamdi Kanu naira biliyan 1 bisa laifin mamaye gidansa a watan Satumban 2017.

Mai shari’a Benson Anya ya bayar da wannan umarni ne a ranar Laraba a lokacin da yake yanke hukunci kan karar da Kanu ya shigar a kan gwamnatin tarayya da sojoji da sauran su.

Alkalin ya kuma umurci gwamnatin tarayya da rundunar soji da su baiwa Kanu hakuri bisa take masa hakkinsa na asali.

Muna tafe da cikakken bayani nan gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here