Wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari, inda suka kashe mutane 21 a ƙaramar hukumar Barkin Ladi da ke jihar Filato.
An kai harin ne a garin Heipang da ke ƙaramar hukumar cikin daren Laraba, wayewar garin ranar Alhamis.
Wani mazaunin Heipang mai suna Julius Pam, wanda harin ya rutsa da ‘yan uwansa ya shaidawa manema labarai yadda lamarin ya kasance.
Ya tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun shigo ne da asubahin ranar Alhamis, inda suka halaka mutane 17 ciki kuwa har da ɗan uwansa, matarsa da kuma yaransu. Wata majiya mai ƙarfi a ofishin rundunar ‘yan sandan jihar ta Filato, ta tabbatar da cewa tuni aka tura jami’ai zuwa yankin da lamarin ya faru.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang, ya ƙaddamar da wata cibiyar tattara bayanai ta tsaro domin bai wa mutane damar sanar da jami’ai halin da suke ciki.
Gwamnan ya ce cibiyar ta samar da wata lambar waya da mutane za su iya kira a kyauta domin ba da bayanai na tsaro a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. Ya ƙara da cewa hakan zai taimakawa gwamnatin jihar wajen samun bayanai da za su ba ta damar ɗaukar matakai na gaggawa a duk lokacin da aka fuskanci wata matsala ta tsaro.