Yadda Na Rubuta Littafin da Zai Taimaka wa Daliban Ilimi Su San Fitattun Magabata da Suka Bayar da Gudummawa a Kano – Kwalli

e55d0842 8b6f 497e b7b1 87f64e55d0bf

Marubuci Kabiru Ahmad Kwalli, daga Kano, ya kammala littafin tarihin fitattun mutanen Kano 24, mai suna “Mu San Magabata”, wanda ya kunshi bayanai kan manyan jaruman da suka taka rawar gani wajen ci gaban al’umma a fannoni daban-daban.

Kwalli ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai da aka gudanar a Mustibrah Polytechnic, Kano, ranar Alhamis, inda ya ce rubuce-rubucen tarihi na bukatar ƙarin kulawa domin adana tarihin mutanen da suka bayar da muhimmiyar gudummawa ga jihar.

Littafin ya yi nazari kan shugabanni, malamai, ’yan kasuwa da masu hidimar jama’a da suka yi suna a tarihi. Daga cikin sunayen da aka ambata akwai:

Madakin Kano Shehu Ahmad, Alƙalin Kano Umaru, Sheikh Sani Auwalu Darma, Alhaji Uba Ringim, Alhaji Imam Wali, Alhaji Ado Dandolo, Malam Nura Alƙali, da Malam Adamu Aminu.

Sauran sun hada da Kansila Malam Ahmadu Rufa’i Daura, Alhaji Barau Maiwake, Alhaji Baballe Ila, Alhaji Baffa Yola, Alhaji Muhammadu Yankwashi Kazaure, Alhaji Mahe Bashir Wali, Alhaji Salisu Sambajo, da Alƙali Husaini Sufi, da sauran fitattu domin cika adadin mutum 24.

Marubucin ya ce wannan juzu’i ne na farko, kuma yana da burin fadada binciken zuwa tarihin malaman addini, sarakunan gargajiya, ’yan kasuwa, matan jarumai da sauran wadanda suka taka muhimmiyar rawa a Kano da Najeriya baki ɗaya.

An kafa kwamitin kaddamar da littafin karkashin jagorancin Farfesa Bashir Yusuf, tare da Alhaji Ibrahim Aminu Dan’lya da Alhaji Ali Adamu a matsayin mataimaka, yayin da Abubakar Farouk Kabara ke matsayin sakatare.

Kwalli ya gode wa dukkan masu goyon baya tare da kira ga al’umma da su karfafa rubuta tarihi domin kare gadon magabata.

A cewar marubucin, za a sanar da ranar kaddamar da littafin a nan gaba kadan bayan kammala shirye-shirye.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here