Matashin ɗan jarida Musa Sani Aliyu wanda aka fi sani da Musa Khan ma’aikacin gidan radio Jalla dake jihar Kano, a daren jiya ya tsallake Wani mumunan hari da barayin waya suka kai masa yayin da yake komawa gida bayan tashi daga wajen aikinsa.
Musa Khan na ɗya daga cikin mambobin Kungiyar Hani da Dakile Kwacen Waya a Jihar Kano (Youth Against Phone Snatching) YAPS.
Rahotanni sun bayyana cewa abun ya faru a kan titin Club Road Kusa da Custom Office yayin da yake tafiya misalin Karfe 9:30 na dare, inda wasu Bata gari akan Babur suka zo masa suka nemi yabada wayar Dake jikin shi, kafin ya zaro daga aljihu dayan ya Fidda Wukar Dake jikin shi Mai Kira ta Musamman ya sare shi a hannu, zafin wannan saran yasa Musa yayi kuwa Domin Neman Taimakon Nan da Nan barayin dasuka ga Jama’a zasu zo sai suka hau Babur dinsu suka gudu
An garzaya dashi asibiti Domin ceto rayuwarshi daga mummunan Yanka da zubar jini da yake.













































