Yaƙi da miyagun Ƙwayoyi: Marwa ya kafa sabbin manufofin ayyukan NDLEA na 2026

WhatsApp Image 2026 01 23 at 10.46.01

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA), Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa Mai ritaya, ya bayyana manyan manufofin ayyukan hukumar na shekarar 2026, inda ya umarci kwamandoji da daraktoci da su ƙara zage damtse wajen tarwatsa manyan ƙungiyoyin fataucin ƙwayoyi tare da faɗaɗa wayar da kan jama’a a faɗin ƙasar.

Marwa ya bayar da wannan umarni ne a yayin taron bita da tsare-tsaren aiki na shekara-shekara da aka gudanar a hedkwatar NDLEA da ke Abuja, wanda ya haɗa manyan jami’an hukumar daga sassa daban-daban, ciki har da kwamandojin jihohi 36 da Abuja, tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa.

A cewarsa, hukumar ta shiga shekarar 2026 da ƙwarin gwiwa, bisa gagarumar nasarorin da ta samu a shekarun baya. Ya bayyana cewa shekarar za ta mayar da hankali ne kan ƙarfafa rage wadatar miyagun ƙwayoyi (DSR) da kuma rage buƙatar su a tsakanin al’umma (DDR).

“Mun samu nasarori masu yawa a baya, amma ba za mu yi sakaci ba. Burinmu a 2026 shi ne katse hanyoyin kuɗin ƙungiyoyin fataucin ƙwayoyi baki ɗaya tare da tabbatar da cewa kowane yanki a Najeriya ya samu isasshen wayar da kai kan illar shaye-shaye,” in ji Marwa.

Ya kuma ja hankalin kwamandoji da su tabbatar da ingantaccen aiwatar da tsare-tsaren aiki, su kasance masu ladabi da kwarewa, tare da gujewa duk wani nau’in sassauci ko sakaci a aiki.

Ya ce dole ne a ƙarfafa sanya ido, tsare-tsare da kuma neman ƙarin taimako a duk inda ƙarfin aiki bai wadatar ba.

Marwa ya ƙara da cewa hukumar za ta ƙara ƙarfafa Kwamitocin Kula da Miyagun Ƙwayoyi na Jihohi, tare da faɗaɗa su zuwa ƙananan hukumomi da mazabu.

Ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa NDLEA za ta ci gaba da kare matasa da iyalai daga barazanar miyagun ƙwayoyi, yana mai kira ga jama’a da su ci gaba da ba da sahihan bayanai domin samun nasara a wannan yaƙi na bai ɗaya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here