Tsofaffin ma’aikatan Radiyon tarayya FRCN sun bayyana a ranar Asabar cewa sun kuduri aniyar shiga zanga-zangar da aka tsara gudanarwa a ranar 8 ga Disamba.
Sakataren kuɗi na ƙasa na tsofaffin ma’aikatan, Bola Popoola, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka fitar a Legas.
Kamfanin dillalancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa, haɗakar kungiyar tsofaffin ma’aikatan tarayya ta ce tana shirye-shiryen gudanar da zanga-zanga a fadin ƙasa domin tabbatar da biyan bashin karin fansho da kuma tallafin jin kai da suke bi.
Popoola ya ce tsofaffin ma’aikatan FRCN a tsarin Fansho na tabbataccen albashi waɗanda ke ƙarƙashin wannan kungiya, ba su da wani zaɓi illa su halarci zanga-zangar domin tabbatar da biyan hakkokinsu.
Ya ce shiga zanga-zangar ya samo asali ne daga rashin biyan su tallafin Naira 25,000 na tsawon watanni shida da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince tun shekarar 2023.
Ya bayyana cewa takwarorinsu da ke ƙasashen waje za su gudanar da irin wannan zanga-zangar a inda suke, domin jaddada matsin lamba kan gwamnati.
Ya ƙara da cewa tsofaffin ma’aikata suna cikin mawuyacin hali duk da cewa sun yi hidima ga ƙasarsu na tsawon shekaru, kuma wannan yanayi na tilasta su neman taimako a tituna yana bukatar gaggawar kulawa.













































