Tinubu ya gana da sabbin shugabannin hafsoshin tsaro

Service Chiefs Tinubu 750x430

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da sabbin shugabannin hafsoshin tsaro a fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Litinin, domin ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa, wannan zama na sirri ya biyo bayan sabbin nade-naden da aka yi a rundunar soji, abin da fadar shugaban ƙasa ta bayyana a matsayin matakin inganta ƙwarewa, tsari da ƙwarin gwiwar jami’an tsaro.

A wajen ganawar akwai shugaban hafsoshin tsaro Janar Olufemi Oluyede, shugaban hafsoshin sojin ƙasa Manjo Janar Waheedi Shaibu, shugaban hafsoshin sojin sama Air Vice Marshal Kennedy Aneke, da kuma shugaban hafsoshin sojin ruwa Rear Admiral Idi Abbas.

Sai dai kawo yanzu ba a bayyana cikakken abin da aka tattauna a taron ba, sai dai ana ganin ganawar ta shafi ƙarin matakan da gwamnati ke shirin ɗauka don ƙarfafa tsarin tsaro a ƙasar.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here