Tattaunawar Sulhu da ƴan Bindigar daji a Katsina na haifar da rashin tsaro a Kano – Kwankwaso ya roƙi Tinubu da ya dauki mataki

WhatsApp Image 2025 11 15 at 15.28.10 750x430

A wani jawabi da ya gabatar a Kano, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta daukar mataki kan karuwar matsalolin tsaro da ake fuskanta a jihar, musamman a yankunan da ke kan iyaka da Katsina.

A yayin taron yaye daliban Skyline University karo na hudu a Kano, Kwankwaso ya bayyana cewa hare-haren da ake samu a kwanakin nan na nuna cewa lamarin tsaro ba abin da za a dauka da wasa ba ne, domin rayuka da dukiyoyi suna cikin hadari.

Yace, Kano ta kasance daya daga cikin jihohin da suka fi samun tsaro a Arewa a tarihi, yayin da yake cewa gwamnati ta zuba jari sosai a lokacinsa wajen shawo kan barazanar Boko Haram da sauran kungiyoyin aikata laifi.

Ya bayyana cewa matsalar ’yan fashin daji ta kara ta’azzara a kan iyakar Kano da Katsina, musamman a kananan hukumomi irin su Tsanyawa, Shanono, Bagwai, Gwarzo da Karaye, inda masu laifi ke ketara iyaka domin aikata barna sannan su koma maboyarsu.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Kwankwaso ya soki yarjejeniyoyin sulhu da ake yi da ’yan fashi a wasu jihohin makwabtaka, yana mai cewa irin wadannan matakan suna ba da damar samun mafaka ga masu aikata laifi ba tare da tsoron hukunci ba.

Ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya ce ke da alhakin kare iyakokin kasa da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi, tare da bayyana cewa matsalar ta samo asali ne daga Zamfara sannan ta bazu zuwa Sokoto, Kebbi da wasu sassan Kaduna, kafin ta fara shafar Kano da Jigawa ta bangaren Katsina.

Kwankwaso ya bukaci gwamnati da ta dauki kwararan matakai domin dakile ’yan fashi da kare al’umma, yana mai gargadin cewa halin da ake ciki na kara tabarbarewa kuma bai kamata a sake game da shi ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here