Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabin bankwana ga ƙasa baki-ɗaya a matsayin na shugaban ƙasa a ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ya fitar, ta ce Buhari zai yi jawabin ne da misalin karfe 7 na safe.
Sanarwar ta kuma buƙaci dukkan gidajen talabijin da radio da kuma sauran kafofin yaɗa labaru na zamani da su nuna jawabin ta hanyar haɗa tashoshinsu da gidan talabijin na ƙasa NTA da kuma gidan rediyon tarayya FRCN.
A ranar Litinin 29 ga watan Mayu ne, shugaba Buhari zai miƙa mulki ga sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu, a daidai lokacin da yake kammala wa’adin mulkinsa karo na biyu na shekara takwas













































