Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya gargadi shugaban hukumar alhazai ta kasa NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh-Usman, da ya daina dabi’ar yin aiki shi ɗaya tilo shugabanni daya tilo musamman wajen tafiyar da al’amuran alhazan Najeriya.
Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan gargadin ne a wata sanarwa da ya aikewa shugaban hukumar ta NAHCON kan zargin karya tsarin sayan kayayyaki, da rashin da’a, da mayar da mambobin hukumar saniyar ware, da nada mataimaka ba bisa ka’ida ba, da dai sauransu.
Gargadin na Shettima na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 17 ga Maris, 2025, mai lamba SH/OVP/DCOS/NAHCON.
Mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, da ke ofishin mataimakin shugaban kasa Sanata Ibrahim Hassan Hadejia ne ya sanya wa wasikar hannu.
Shettima ya fusata da salon yadda shugaban NAHCON ke kafa kwamitoci domin yanke hukunci a madadin hukumar wanda ya sabawa dokar hukumar.
Labari mai alaƙa: Rikici ya sake ɓarkewa a hukumar NAHCON
Gargadin na zuwa ne kwanaki kadan bayan da mambobin hukumar NAHCON suka kai kara ofishinsa kan wani babban rashin da’a da suke zargin Farfesa Abdullahi Sale Usman ke yi.
SolaceBase ta ruwaito cewa koken mai shafi shida, mai kwanan ranar 13 ga Maris, 2025 mai taken, “Cire mu da gangan daga ayyukan sa ido,” ta samu sa hannun kwamishinonin NAHCON guda takwas wadanda ba na dindindin ba da ke wakiltar shiyoyin siyasa shida da Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, NSCIA, da Jama’atul Nasril Islam, JNI.
Sun zargi Farfesan da cire su daga ayyukan da doka ta tanada a hukumar.
Wadanda suka rattaba hannu kan koken sun hada da Farfesa Muhammad Umaru Ndagi (Arewa ta tsakiya), Alhaji Abba K. Jato (Arewa maso Gabas), Shaykh Muhammad Bn Uthman (Arewa maso Yamma), Hajiya Aishat Obi (Kudu maso Gabas), Zainab Musa (Kudu-Kudu), Dokta Tajudeen Abefe Oladejo (Kudu maso Yamma), Farfesa Adedimeji Mahfouz (Kudu maso Gabas), Farfesa Adedimeji Mahfouz (Kudu maso Gabas), Farfesa Adedimeji MahfouzNI (Mahfouz) Inuwa.
Tun da farko dai kungiyar manyan ma’aikatan gwamnati a Najeriya ta zargi hukumar NAHCON da nuna bangaranci da rashin adalci na sanya jami’an a kan aikin hukumar.













































