Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa za ta ci gaba da tsaurara aiwatar da dokar hana zirga-zirgar achaba da kuma takaita yawon dare na adaidaita sahu a yankunan da gwamnati ta kayyade domin inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a cikin birni.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a madadin kwamishinan ’yan sanda Ibrahim Adamu Bakori, ta tabbatar da cewa dokar ta ci gaba da aiki a kananan hukumomi tara da suka haɗa da Kano Municipal, Gwale, Dala, Fagge, Nassarawa, Tarauni, Kumbotso da kuma sassan Ungogo da Dawakin Kudu kamar Jido, Tambuwal da Gurjiya.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa rundunar ’yan sanda ta bayyana cewa matakan suna da nufin ƙarfafa tsaro, rage laifuka da kuma hana yaduwar bayanan da ba su da tushe waɗanda ka iya tayar da hankalin jama’a a wasu lokuta.
Rundunar ta yi gargadin cewa duk wani mutum da ya karya umarnin ta zai fuskanci hukunci bisa tanadin doka.
Karanta: Gwamnan Kano ya musanta jita-jitar barazanar tsaro a jihar
Ta kuma bukaci al’umma su bi ka’idojin da aka shimfiɗa tare da ba da hadin kai ga jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin jihar.
Rundunar ta jaddada muhimmancin bayar da rahoton duk wani motsi ko abin da ake zargin zai iya zama barazana ga tsaro.
A cewar rundunar, aikin aiwatar da wannan doka zai kasance ne cikin haɗin gwiwa tsakanin jami’an ’yan sanda da hukumar kula da zirga-zirga ta jihar Kano, tare da tabbatar da cewa dokar ta tabbata a dukkan yankunan da aka ayyana domin hakan ya taimaka wajen kare lafiyar jama’a.
Rundunar ’yan sandan ta bayyana cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakai na tabbatar da tsaro, inda dokokin nan gaba za su fi mayar da hankali kan kare al’umma daga duk wata barazana ta rashin tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma.













































