Rundunar ƴan sandan Najeriya ta gano jami’anta da wani faifan bidiyo ya nuna suna karɓar kuɗi a hannun ƴan China

Police Police Chinese 750x430

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis ta ce za ta hukunta jami’anta da aka kama a wani faifan bidiyo da ya nuna suna karbar kudade daga hannun ‘yan kasar China.

A cikin faifan bidiyon, an ga wasu ‘yan kasar China suna raba kudin Naira ga ‘yan sandan Najeriya a cikin jerin gwano. Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda ‘yan Najeriya da dama ke nuna rashin jin dadinsu tare da yin kira da a kawo gyara a cikin rundunar.

Bidiyon ya nuna a daidai lokacin da jami’an, dauke da makamai, sanye da kayan yaki, suka karbi kudade daga hannun ‘yan kasashen ketare.

Da yake nuna damuwarsa kan lamarin, mai magana da yawun rundunar, Muyiwa Adejobi, ya yi Allah-wadai da halin da jami’ansu suka nuna, inda ya bayyana abin da suka yi a matsayin rashin da’a.

Ya jaddada kudirin rundunar na tabbatar da kwarewa da kuma rike amanar jama’a.

Ko da yake bai bayyana yanayin hukuncin da za a yi musu ba, sai dai ya tabbatar wa jama’a cewa za a yi adalci.

Rundunar ta gargadi mutane da kungiyoyi masu amfani da ayyukan ‘yan sanda, musamman masu rakiya da masu gadi da su guji irin wannan dabi’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here