Ramadana: NDLEA ta kai samame maboyar miyagun ƙwayoyi a Kano, ta kama mutane 19

NDLEA 1

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), shiyyar Kano, ta kama mutane 19 tare da rusa wasu maboyar miyagun ƙwayoyi a unguwar Gezawa, a wani mataki na dakile ayyukan fataucin miyagun ƙwayoyi a lokacin azumin Ramadana da ma bayan sa.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Sadiq Muhammad-Maigatari, ya fitar a ranar Alhamis a Kano.

Muhammad-Maigatari ya ruwaito Kwamandan Jiha na hukumar, Dahiru Yahaya-Lawal, yana cewa an gudanar da samamen ne a matsayin ɓangare na shirin da suke aiwatarwa mai taken “Operation Ramadan Mubarak”.

Ya ce manufar samamen ita ce kare lafiyar jama’a da kuma kiyaye tsarkin watan Ramadana.

Kakakin ya ƙara da cewa an gudanar da aikin ne bayan samun sahihan bayanai daga wani mazaunin yankin, inda aka kwato miyagun ƙwayoyi daban-daban.

Ya ce abubuwan da aka kama sun haɗa da tabar wiwi, diazepam, Exol-5 (wanda aka fi sani da madarar sukudaye “Suck and Die”), ƙwayoyin pregabalin da sauran ƙwayoyi da aka haramta.

Ya ƙara da cewa duk abubuwan da aka kwato suna hannun NDLEA, yayin da ake ci gaba da bincike.

Ya ce manufarsu ita ce tabbatar da tituna sun kasance cikin aminci domin jama’a su gudanar da azumi cikin kwanciyar hankali.

Ya gargaɗi cewa duk wanda ya yi watsi da addininsa, lafiyarsa da kuma tsaron sauran jama’a, hukumar za ta ɗauki matakin da ya dace domin kare al’umma.

Kwamandan ya yabawa jama’a bisa ba da bayanai masu amfani, tare da ƙarfafa su su ci gaba da ba da haɗin kai wajen yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.

Ya ce aikin ya yi daidai da umarnin shugaban hukumar na ƙasa, Mohamed Buba-Marwa mai ritaya, na ci gaba da ƙarfafa yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasa.

Yahaya-Lawal ya sake tabbatar da aniyar rundunar Kano na ɗaukar matakai na gaba-gaba tare da haɗin gwiwar al’umma domin rusa hanyoyin fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma hukunta masu laifi.

Ya kuma buƙaci mazauna yankin da su rika kai rahoton duk wani motsi ko harkar miyagun ƙwayoyi da suka gani, yana mai cewa bayanai a kan lokaci na da matuƙar muhimmanci wajen kare lafiyar al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here