Ramadan: Farashin ƙwai ya yi tashin gwauron zabi a Kano, inda ya kai Naira 8,500 kan kowanne kiras

Eggs Crates

Farashin ƙwai a Kano ya yi tashin gwauron zabi bayan fara azumin watan Ramadan, inda yanzu kiras ɗaya ake sayarwa kan Naira 8,500, sabanin Naira 6,000 zuwa Naira 6,500 da ake sayarwa kafin watan azumi.

Ziyarar da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya kai kasuwannin Sabon-Gari da Yankaba ta nuna cewa farashin ya ƙaru duk da yawan buƙatar da ake da ita a wannan lokaci.

Masu sayar da ƙwai sun danganta tashin farashin da ƙarin buƙata a lokacin Ramadan, inda iyalai da dama ke amfani da ƙwai wajen buɗa baki.

Musa Sani, wani mai sayar da ƙwai a kasuwar Yankaba, ya ce tashin farashin ya samo asali ne daga ƙarancin ƙwai da ake samarwa a cikin gida, lamarin da ya ƙara tsananta sakamakon matsalolin tattalin arziki da ke addabar harkar kiwon kaji.

Nasiru Ali, wani dillali a kasuwar Sabon-Gari, ya ce hauhawar kuɗin kiwon kaji, sayen abinci da kula da gonaki na daga cikin abubuwan da suka janyo ƙarin farashin.

Wani mai sayarwa a Zoo Road ya ce kafin Ramadan ana samun ƙwai a sauƙaƙe kuma farashi yana daidaito, amma yayin da watan azumi ya karato, wadatar ta ragu farashi kuma ya fara tashi.

Ya ƙara da cewa ƙwai da ake sayarwa kan Naira 200 kowanne yanzu ya kai tsakanin Naira 280 zuwa Naira 300.

Shugaban Ƙungiyar Masu Sayar da Ƙwai a kasuwar Dakata, Abdulsalam Mudi, ya tabbatar da cewa haɗuwar ƙarancin ƙwai da yawaitar buƙata a watan Ramadan ne ya haddasa wannan tashin farashi.

Wani mai saye, Nura Imam, ya nuna damuwa kan yadda farashi ke tashi a lokutan bukukuwa, tare da kira ga hukumomi da masu ruwa da tsaki da su tallafa wa manoman kaji domin samar da wadataccen ƙwai a lokacin azumi da ma bayan sa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here