Nijar da Mali da Burkina Faso za su samar da dakarun ƙawance na yaƙar masu ikirarin jihadi

Nijar, Mali, Burkina Faso, dakaru, jihadi, ƙawance
Ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso sun ce za su kafa wata rundunar haɗin gwiwa don yaƙar masu iƙirarin jihadi da ke yi wa ƙasashen barazana.Shugaban...

Ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso sun ce za su kafa wata rundunar haɗin gwiwa don yaƙar masu iƙirarin jihadi da ke yi wa ƙasashen barazana.

Shugaban dakarun sojin Nijar, Moussa Salaou Barmou ya ce nan ba da jimawa ba rundunar za ta fara aiki, to sai dai bai yi cikakken bayanin girman rundunar ba.

Moussa Salaou Barmou ya bayyana hakan ne a gidan talabijin ranar Laraba, jim kaɗan bayan taron da ƙasashen suka yi game da batun a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar.

Karin labari: Kano Leads ta yi kira ga gwamnatin Kano ta samar da wadatattun gurin zubar da shara a jihar

ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi da ke da alaƙa da al-Qaeda sun kashe dubban mutane a yankin cikin shekarar da ta gabata.

A ‘yan watan nin baya-bayan nan shugaban nin sojin da ke mulkin ƙasashen uku na ƙara zama manyan aninan juna.

Karin labari: Majalisar dokokin Edo ta fara shirin tsige Shaibu

A watan Satumbar shekarar da ta gabata, suka kafa ƙungiyar hadin kan Ƙasashen Yankin SahelAES, inda suka fice daga ƙungiyoyin ƙawancen ‘international force‘ da G5 da aka kafa don yaƙar masu ikirarin jihadi a yankin.

A shekarun baya-bayan nan matsalar tsaro na ƙara ta’azzara a yankin Sahel da ke Yammacin Afirka, duk kuwa da alƙawuran magance matsalar da sojojin da ke mulkin ƙasahen suka sha yi.

Ƙasashen uku dai sun yanke alaƙarsu da Faransa, tsohuwar uwar gijiyarsu, wadda dakarunta suka kwashe shekaru da dama suna aiki a ƙasashen.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here