NELFUND ta sanar da lokacin buɗe shafin neman tallafin karatu na shekarar 2025/2026

NELFUND 750x430

Hukumar bada tallafin bashin na karatu a Najeriya (NELFUND) ya bayyana cewa zai sake buɗe shafin neman tallafi ga sabbin ɗalibai a mako na biyu na watan Oktoba 2025, domin shekarar karatu ta 2025/2026, kuma zai kasance a buɗe har zuwa watan Janairu 2026.

A cikin sanarwar da daraktan sashen yada labarai na NELFUND, Misis Oseyemi Oluwatuyi ta sanya hannu a ranar Litinin, hukumar ta ce an rufe shafin neman tallafin shekarar 2024/2025 daga ranar Talata, 30 ga Satumba 2025.

NELFUND ta ce wannan mataki na nuni da ƙarshen zangon karatu na biyu tun fara shirin, tare da bawa hukumar damar kammala tantance aikace-aikace da kuma ci gaba da biyan kuɗaɗen ɗalibai.

An shawarci makarantun da ba su fara sabon zangon karatu ba cikin lokacin da aka tsara, da su sanar da hukumar domin samun sauƙi.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa duk wani ɗalibi a shekarar 2024/2025 bai samu sahalewa daga makaranta ba kafin ranar 8 ga Oktoba 2025, za a soke shi kai tsaye.

Hakan na nufin waɗanda abin ya shafa dole ne su sake neman tallafi daga shekarar 2025/2026.

Hukumar ta kuma ce akwai ɗalibai da ba su samu amincewa ko biyan tallafi ba a wannan zango, saboda makarantun su ba su kammala sahalewa ba.

NELFUND ta ce tana ci gaba da tattaunawa da irin waɗannan makarantu, amma za ta wallafa sunayen waɗanda suka ƙi bin doka don jama’a su sani.

Game da kuɗaɗen kula da ɗalibai, NELFUND ta ce za a ci gaba da biyan na shekarar 2024/2025 har zuwa watan Nuwamba 2025, amma duk wani ɗalibi zai sake neman tallafi domin shekarar 2025/2026 idan har zai ci gaba da samun cancanta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here