Na kusa haƙura sa takarar shugaban kasa a 2023 – Tinubu

Tinubu Iftar 750x430

Shugaba Bola Tinubu ya ce ya kusa hakura daga takarar shugaban kasa a 2023.

Shugaban ya bayyana haka ne a wani buda baki na musamman da aka gudanar a fadar shugaban kasa a daren Asabar.

Shugaba Tinubu ya godewa bakin da suka halarta, da addu’o’insu, da kuma gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban kasa, ya kuma yabawa ‘yan Nijeriya bisa yadda suka yi ta addu’o’i yayin da ya cika shekaru 73 a duniya.

Da yake waiwaye a tafiyarsa ta siyasa, shugaba Tinubu ya bayyana wani lokaci da ya samu shakku a yakin neman zaben 2023 a lokacin da yake tunanin janyewa daga takarar bayan ya gana da wani dan uwansa na kusa inda yake bukatar Naira dubu 50 don sayen kayan abinci.

Shugaban ya bayyana cewa daga baya kawun nasa ya buga waya ya tabbatar da karbar kudin amma ya amince cewa ya baiwa dan aiken naira 10,000 ne kawai, ya ajiye sauran.

Shugaba Tinubu ya yi nuni da cewa, ya karbi mulki ne a lokacin da ake fama da rashin tabbas a fannin tattalin arziki, kuma dole ne ya yi gaggawar yanke shawara ta ɗaukan mataki ciki har da cire tallafin man fetur.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here