Majalisar ƙaramar hukumar Kirikasamma ta jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya da kuma jikkatar wasu bakwai sakamakon rushewar wani gini a yankin.
Jami’in yaɗa labaran hukumar, Musa Muhammad, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a Dutse ranar lahadi.
Ya ce lamarin ya faru ne bayan ruwan sama mai yawa da aka samu a Kirikasamma da kewaye, inda ginin ya rushe a ƙauyen Kabak da tsakar dare ranar juma’a.
Karin karatu: Hukumar NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane 231, sama da 600 sun ji rauni sakamakon ambaliyar a 2025
Muhammad ya bayyana cewa mutum bakwai sun jikkata sosai, yayin da mutum ɗaya ya rasa ransa.
Cikin waɗanda suka jikkata, biyar an kwantar da su a asibiti don samun kulawa, yayin da aka sallami sauran biyu bayan samun magani.
Ya ƙara da cewa shugaban ƙaramar hukumar, Muhammad Maji, ya ziyarci wurin da abin ya faru don jajanta wa waɗanda abin ya shafa, tare da nuna goyon bayansa.
Hakazalika, shugaban ya bayar da tallafin naira dubu dari biyar domin kula da jinyar waɗanda suka jikkata da kuma naira dubu ɗari guda don taimakon gaggawa ga iyalan wanda suka rasa ransu.













































