Ministan babban birnin tarayya Abuja ya musanta labarin da ya yadu a kafafen sada zumunta da wasu gidajen yada labarai cewa an bayar da umarnin rufe dukkan makarantun gwamnati a Abuja daga ranar 28 ga Nuwamba, 2025.
Ya bayyana cewa wannan jita-jita ba ta da tushe, don haka aka umurci iyaye, dalibai da hukumomin makarantu da su yi watsi da ita domin tsarin jadawalin karatu bai sauya ba.
A cikin sanarwar da mai taimaka wa Ministan Abuja kan harkokin yada labarai da kafafen sada zumunta, Lere Olayinka, ya fitar, ta bayyana cewa rahoton yaudara ne da ba shi da dangantaka da gaskiya.
Hakan ne ya sa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya dakatar da Sakataren ilimi Dakta Danlami Hayyo, saboda takardar da aka fitar ba tare da izini ba ta janyo rudani.
Haka kuma an umarci shugabar ma’aikata, Hajiya Nancy Sabanti Nathan, da ta dauki mataki kan Daraktar Ayyukan Makarantu, ita kuwa Hajiya Aishatu Sani Alhassan, ta sanya ido domin bin ka’idojin aiki.
Gwamnatin ta kara tabbatar da cewa babu wani mataki da aka dauka na rufe makarantu a kowanne mataki, tare da jaddada cewa iyaye da dalibai su ci gaba da harkokin makaranta yadda aka saba.
Ta kuma ce Ministan ya umurci dawo da shirin Operation Sweep da wasu tsare-tsaren tsaro domin kara tabbatar da kariya a makarantun Abuja.
Dakta Hayyo, wanda aka dakatar, yayin amsa tambayoyin ’yan jarida, ya musanta cewa ya san da takardar da aka fitar, wanda ya ce shi ma daga kafafen sada zumunta ya gani.
Ya bayyana cewa ikon rufe makarantu yana hannun Ministan Abuja ne kawai, kuma babu wani dalili da ya dace da rufe makarantu kafin ranar 28 ga watan.
Ya tabbatar wa iyaye cewa ba a samu wata matsala ta tsaro ko ta gudanarwa ba da za ta iya kawo dakatar da karatu, tare da jaddada cewa Abuja na cikin kwanciyar hankali, kuma harkokin koyarwa da koyo suna gudana yadda ya kamata ba tare da wata tangarda ba.












































