Majalisar Wakilai, ta amince da Naira tiriliyan huɗu da aka ware na tallafin man fetur.
Amincewar ta biyo bayan buƙatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi na sake fasalin kasafin kuɗin baɗi.
Yayin miƙa buƙatar sake duba tsarin kashe kuɗaden, shugaba Buhari ya buƙaci ƴan majalisar da su amince da ƙarin naira tiriliyan 3 da biliyan 557 baya ga naira biliyan 442 da miliyan 72 da aka tanadar a cikin kasafin kuɗin bana a tallafi matsayin tallafin mai.
Majalisar ta kuma amince da rage yawan ɗanyen mai da ake hakowa daga ganga miliyan 1 da dubu ɗari takwas a kowace rana zuwa ganga miliyan 1 da dubu ɗari shida a kowace rana da kuma ƙimar farashin dala 73 a kowacce ganga.
Majalisar ta kuma amince da rage tanadin ayyukan da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa da kusan naira biliyan 200 daga naira biliyan 352 da miliyan tamanin.













































