Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Honorabul Khalid Ishaq Diso, na tsawon watanni uku.
Majalisar ta ɗauki wannan mataki ne yayin da ta amince da rahoton kwamitin kula da harkokin kananan hukumomi da naɗe-naɗen sarauta a zamanta na ranar Talata.
A cewar majalisar, shida daga cikin Kansilolin ƙaramar hukumar Gwale, da mambobi 10 ne suka shigar da ƙorafin abin da Ciyaman ɗin yake aikata wa.
A jawabin shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Honorabul Yusuf Isma’il Falgore, ya ce ana zargin ciyaman ɗin da yanke hukunci bisa ra’ayin kansa ba tare da tuntuɓar kansiloli ba.













































