Ma’aikatan lafiya sun dakatar da yajin aikin ƙasa baki ɗaya na kwanaki 84 da suka yi

doctors

Haɗaɗɗiyar ƙungiyoyin ma’aikatan sashen lafiya ta ƙasa JOHESU a ranar Juma’a ta sanar da dakatar da yajin aikin ƙasa baki ɗaya da ta shafe kwanaki 84 tana yi, bayan cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban JOHESU na ƙasa Kabiru Ado-Minjibir da sakataren ƙasa Martin Egbanubi suka sanya wa hannu a birnin Abuja.

Ƙungiyar ta bayyana cewa an cimma wannan matsaya ne bayan shawarwarin da aka cimma a taron gaggawa na babban kwamitin zartarwa na ƙasa NEC.

An gudanar da taron ne domin duba sakamakon taron sasanci da aka yi da gwamnatin tarayya a ranar 5 ga Fabrairu a ma’aikatar kwadago da ayyukan yi.

Sanarwar ta nuna cewa muhimman matsayai da aka cimma sun haɗa da fara tattaunawar yarjejeniyar haɗin gwiwa ta aiki CBA da kuma bai wa batutuwan da suka shafi daidaita tsarin albashin ma’aikatan lafiya CONHESS fifiko nan take.

An kuma bayyana cewa yarjejeniyar ta tanadi ware kuɗi a kasafin kuɗin shekarar 2026 domin aiwatar da daidaiton albashi bisa tsarin da kwamitin fasaha ya tanada tun farko.

Gwamnatin tarayya ta kuma amince da janye umarnin “ba aiki ba biya” da ta sanya wa mambobin JOHESU a lokacin yajin aikin.

Sanarwar ta ƙara da cewa za a biya albashin watan Janairu na shekarar 2026 ga dukkan mambobin JOHESU nan take, tare da tabbatar da cewa babu wani mamba da za a tsangwama, hukuntawa ko razana saboda shiga yajin aikin.

Bayan duba matsayar da aka cimma, kwamitin zartarwa na ƙasa NEC ya amince baki ɗaya da dakatar da yajin aikin ƙasa baki ɗaya na dindindin.

Daga nan kwamitin ya umarci dukkan mambobin JOHESU a cibiyoyin lafiya na tarayya da na jihohi da su koma bakin aiki nan take.

Ƙungiyar ta bayyana cewa yajin aikin da ya fara a ranar 15 ga Nuwamba 2025 ya samo asali ne daga gazawar aiwatar da daidaiton albashin CONHESS da sauran batutuwan jin daɗin ma’aikata da suka jima suna jiran warwarewa.

A cewar ƙungiyar, tsawaita yajin aikin ya yi matuƙar illa ga hidimar kiwon lafiya, lamarin da ya haifar da ƙaruwa a mace-macen mata masu juna biyu da jarirai a fadin ƙasar.

An kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yi asarar kusan Naira Tiriliyan ɗaya a lokacin yajin aikin.

Ƙungiyar ta ce an kira taron sasancin ne ta hannun ma’aikatar kwadago da ayyukan yi bayan wa’adin kwanaki 14 da ƙungiyoyin NLC da TUC suka bai wa gwamnatin tarayya.

Taron ya samu halartar ministocin kwadago, kuɗi da lafiya, tare da wakilan hukumar albashi da kudaden shiga ta ƙasa.

Sai dai ƙungiyar ta yaba da rawar da shugabannin majalisar dokoki ta ƙasa, sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin ƙwararru suka taka wajen warware rikicin.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatocin tarayya da jihohi da su cika dukkan yarjejeniyoyin da aka cimma domin kauce wa sake afkuwar yajin aiki a nan gaba. Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here