Kotun koli ta tabbatar da Kakakin majalisar dokokin jihar Delta, Sherrif Oborevwori, a matsayin sahihin dan takaran gwamnan jihar karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Kwamitin Alkalan karkashin jagorancin Amina Augie a ranar Juma’a ya ce hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a baya daidai ne. David Edevbie, ya shigar da kara kotu ne bayan zaben fidda gwanin gwamna a jihar.
Sheriff Oborevwori ya samu kuri’u 590 yayinda David Edevbie ya samu kuri’u 113. Yayinda gwamnan jihar Ifeanyi Okowa ke goyon bayan Sheriff, tsohon gwamna James Ibori na goyon bayan Edevbie.













































