Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa tsohon janar na soja tare da umartar mayar da sama da Naira Biliyan 4

Court of Appeal 750x430 (1)

Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa tsohon babban daraktan rukunin gudanarwa na Kamfanin Kula da Kadarorin Rundunar Sojin Najeriya (NAPL), Manjo Janar Umar Mohammed, kan laifin satar kudi da karkatar da kudaden kamfanin.

A cikin sahihin kwafin hukuncin kotun, kotun daukaka kara ta yi watsi da karar daukaka kara da Mohammed ya shigar yana kalubalantar hurumin kotun soji ta musamman ta rundunar sojin Najeriya da kuma sahihancin hukuncin da ta yanke.

Tun farko kotun sojin ta same shi da laifi tare da yanke masa hukunci a ranar 10 ga Oktoba 2023 kan laifukan da suka shafi satar kudi da kuma karkatar da kudaden kamfanin Nigerian Army Properties Limited.

Bayan hukuncin, an kore Mohammed daga rundunar sojin Najeriya, sannan aka yanke masa hukuncin daurin kurkuku tare da umartar sa ya mayar da Dala 2,099,700 da kuma Naira Biliyan 1.65 ga kamfanin.

Bai gamsu da hukuncin ba, sai ya shigar da kara a kotun daukaka kara a ranar 12 ga Fabrairu 2025 yana cewa hukuncin da aka yanke masa bai samu isasshiyar hujja mai inganci ba.

Kwamitin alkalai uku na kotun da suka hada da Abba Mohammed, Okon Abang da Eberechi Nyesom-Wike sun yi watsi da karar tare da bayyana cewa hujjojin da aka gabatar a kotun sojin sun tabbatar da aikata laifukan.

A cikin hukuncin da aka fitar a ranar Litinin, kotun ta bayyana cewa kotun sojin ta yi daidai da ta yi watsi da bayanin kare kai na tsohon janar din saboda rashin daidaito da rashin sahihanci.

Kotun ta lura da sabani a cikin bayanansa musamman ikirarin da ya yi cewa kamfanin bai taba gudanar da ayyukan jiragen ruwa a tashar jiragen ruwa ba, alhali wasu takardu da shi da kansa ya rubuta sun nuna akasin haka.

Alkalai sun bayyana cewa irin wadannan sabani sun lalata amincin bayanansa.

Saboda haka kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da kuma daurin da kotun sojin ta yanke kan dukkan tuhume-tuhumen sai dai wadanda suka shafi jabun takardu.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa a watan Agusta 2025 mai shari’a Dehinde Dipeolu na babbar kotun tarayya da ke jihar Legas ya kuma bayar da umarnin kwace hannayen jari da darajarsu ta haura Naira Biliyan 5 da aka gano suna da alaka da Mohammed da wani dan kasuwa mai suna Kayode Filani.

An bayar da wannan umarni ne bayan wata bukata da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gabatar inda ta bayyana cewa hannayen jarin guda 245,568,137 an saye su ne da kudaden da aka samu ta haramtattun ayyuka a lokacin da Mohammed yake jagorantar kamfanin kadarorin rundunar sojin.

Lauyar EFCC a shari’ar, Hanatu Kofar Naisa ta bayyana cewa kotun sojin ta riga ta same shi da laifi kan tuhume-tuhume 14 cikin 18 da suka shafi satar kudi da sauran laifuka masu alaka.

Ta kuma kara da cewa hukumar ta cika dukkan sharuddan doka da suka dace domin kwace dukiyar har abada ciki har da sanarwar da aka buga a jaridu ba tare da wani ya kalubalanta ba.

Lokacin da yake amincewa da bukatar, mai shari’a Dipeolu ya bayyana cewa EFCC ta tabbatar da shari’arta, tare da bayar da umarnin kwace hannayen jarin har abada ga gwamnatin tarayya domin amfanin kamfanin.

An gabatar da wannan bukata ne karkashin sashe na 44(2)(b) na kundin tsarin mulkin shekarar 1999 da kuma sashe na 17 na dokar “Yaƙi sa Zamba Ta Kudin Gabatarwa da Sauran Laifukan Damfara Masu Alaka.” ta shekarar 2006. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here