Kotun daukaka kara ta dage shari’ar babban taron PDP na Ibadan ba tare da saka ranar ci gaba ba

PDP PDP 750x430 (1)

Kotun daukaka kara da ke Ibadan ta dage sauraron karar da bangarori biyu na jam’iyyar PDP suka shigar kan babban taron jam’iyyar da aka gudanar a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba a Ibadan ba tare da sanya ranar da za a ci gaba ba.

Babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan ya fitar da Alhaji Tanimu Turaki a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa, yayin da Alhaji Mohammed AbdulRahman ke jagorantar wani bangare na jam’iyyar.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa bangaren AbdulRahman Mohammed ya samu hukunci daga babbar kotun tarayya da ke Ibadan wanda ya soke sakamakon babban taron jam’iyyar da aka gudanar a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba na shekarar 2025 a Ibadan.

Sai dai a wata kara ta daban da bangaren Tanimu Turaki ya shigar, Mai shari’a Ladiran Akintola na babbar kotun jihar Oyo ya yanke hukuncin cewa babban taron PDP na Ibadan ya cika duk sharuddan kundin tsarin mulkin jam’iyyar da kuma dokar zabe.

Bayan haka bangarorin biyu na jam’iyyar suka shigar da daukaka kara daban-daban a kotun daukaka kara da ke Ibadan.

NAN ya kuma rawaito cewa kotun daukaka karar ta umurci bangarorin biyu a ranar Juma’a da su fara kokarin sasanta rikicin cikin lumana bayan ta karbi bukatar bangaren Turaki na janye daukaka karar da ya shigar.

A zaman kotun na ranar Laraba, alkalai uku na kotun daukaka kara karkashin jagorancin Mai shari’a Biobele Georgewill sun tambayi bangarorin yadda kokarin sasanta rikicin cikin lumana ke tafiya.

Karanta: PDP ɓangaren jagorancin Turaki ya ki amincewa da hukuncin kotun daukaka kara, zai tafi kotun koli

Lauyan PDP, Mista Musibau Adetunbi SAN da Mista Jimoh Mumini SAN sun shaida wa kotu cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin domin cimma matsaya kan lamarin.

Sunday Ameh SAN, lauyan Alhaji Mohammed AbdulRahman da Sanatoci Samuel Anyanwu da Mao Ohuabunwa, ya bayyana wa kotu cewa ya tattauna da wadanda yake wakilta kuma sun amince da sasanta lamarin cikin lumana.

A nata bangaren, Misis F. Ajiboye, lauyan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta ce hukumar na son bangarorin su sasanta rikicin cikin lumana.

Mai shari’a Georgewill ya bayyana cewa kotu ta dage sauraron shari’ar ba tare da sanya ranar ci gaba ba saboda bangarorin sun nuna aniyarsu ta sasanta lamarin.

Ya kuma bukaci bangarorin su yi gaggawa domin jadawalin zabe na INEC ba zai jira su ba.

Kotun ta kuma bukaci lauyoyin da ke cikin shari’ar su ba wadanda suke wakilta shawarar doka yadda ya kamata, tare da nuna cewa nasarar sasanta rikicin ko akasin haka ne zai tantance makomar jam’iyyar.

Mai shari’a Georgewill ya kara da cewa kotun ta san da wani hukunci da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke a kan wannan batu, kuma da za ta tura karar zuwa Abuja idan bangarorin ba su sanar da kotun cewa suna son sasanta rikicin ba.

Ya bukaci bangarorin su sanar da kotu da zarar sun cimma matsaya kan sharuddan sasanci ko kuma akasin haka domin kotun ta sanya ranar ci gaba da sauraron shari’ar.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here