A karshen makomnan ne wani mummunan hatsari ya wakana a kauyen Hawan Jaki dake kan titin Alkaleri zuwa Gombe a karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi inda mutane 11 suka mutu.
Kwamandan hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta kasa a jihar Bauchi Mista Yusuf Abdullahi ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa mutane 8 ne suka samu munanan raunuka a hadarin.
Ya ce hatsarin ya hada da motar ‘yan kasuwa guda daya ta Yankari Express dake jigilar sifiri da kuma wata mota kirar Dangote.
Abdullahi ya alakanta musabbabin hadarin da tuki mai tsananin gudu da motocin keyi hakan ya sanya faruwar hatsarin.
“Akalla kimanin maza 20 ne mummunan hadarin motar ya rutsa da su. Tara daga cikinsu sun rasa rayukansu nan take yayin da biyu kuma jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsu a babban asibitin Alkaleri.
“Rahoton yace wasu takwas kuma sun samu raunuka daban-daban, ayayin da suke cigaba da karbar magani a asibitin Alkaleri inda aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu,” inji shi.
Abdullahi ya shawarci masu ababen hawa da su rika kiyaye ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa a koda yaushe yayin da suke tafiya.













































