Kano ta samu kashi 51.9 na yara masu ƙarancin girma, ƙwararren likitan cimaka ya yi gargaɗi

Malnutrition in Kano cc

Shugaban ƙungiyar ƙwararrun masana ilimin abinci ta ƙasa reshen Jihar Kano, Dakta Auwal Musa Umar, ya nuna damuwa matuƙa kan yadda matsalar rashin ingantaccen abinci mai gina jiki ke ƙaruwa a Jihar Kano, inda ya buƙaci gwamnati, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa kai domin tunkarar matsalar cikin gaggawa.

Dakta Umar ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da jaridar Solacebase, inda ya bayyana cewa rashin ingantaccen abinci na daga cikin manyan matsalolin lafiyar jama’a da ke addabar yara a jihar, musamman waɗanda ke ƙasa da shekaru biyar.

Ya bayyana cewa wannan matsala na da illa mai tsanani ga rayuwar yara da makomarsu.

A cewar sa, ƙungiyar ƙwararrun masana ilimin abinci ƙungiya ce ta ƙwararru da ke haɗa masana abinci da masu kula da tsarin ciyarwa daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa yana aiki a ma’aikatar lafiya ta Jihar Kano a matsayin babban jami’in kula da abinci mai gina jiki da kuma mataimakin jami’in wayar da kan jama’a kan harkokin lafiya.

Da yake bayani kan ma’anar ilimin abinci, Dakta Umar ya nuna cewa ilimi ne na kimiyya da ke nazarin yadda jiki ke karɓar abinci, narkar da shi, shaƙa da kuma amfani da shi domin kiyaye lafiya.

Ya jaddada cewa samun daidaitaccen abinci na buƙatar wadataccen sinadarai masu gina jiki da ƙananan sinadarai, inda duk wata rashi ko yawa ko rashin daidaito ke haifar da matsalar rashin ingantaccen abinci.

Ya rarraba matsalar rashin ingantaccen abinci zuwa nau’i biyu, wato ƙarancin abinci mai gina jiki da kuma yawan sa fiye da kima, inda ya bayyana cewa ƙarancin abinci ne ya fi kamari a Jihar Kano.

Ya ce yara da dama na fama da tangardar girma, raunannan jiki da ƙarancin nauyi, abubuwan da ke haifar da illa mai ɗorewa ga girman jiki, bunƙasar kwakwalwa da aikin sassan jiki gaba ɗaya.

Dakta Umar ya kawo bayanai daga binciken ƙididdigar yawan jama’a da lafiyar iyali na ƙasa na shekarar 2023 zuwa 2024 wanda ya nuna cewa kashi 51.9 na yara ƙasa da shekaru biyar a Jihar Kano na fama da tangardar girma, idan aka kwatanta da kashi 12.1 a Jihar Rivers.

Ya bayyana wannan adadi a matsayin abin firgici kuma shaida ce ta tsananin ƙarancin abinci mai gina jiki a jihar.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa ya kuma danganta haddasa matsalar da ƙarancin ilimin abinci, ruwan sha mara tsabta da rashin tsafta.

Ya bayyana cewa ko da akwai abinci, gidaje da dama ba sa cin daidaitaccen abinci, inda suke haɗa nau’o’in abinci daga rukuni ɗaya maimakon haɗa furotin, kayan lambu da ’ya’yan itatuwa.

Ya ƙara da cewa bunƙasa harkokin noma, inganta wayar da kai kan ilimin abinci da ɗaukar ƙwararrun masana na daga cikin muhimman matakai da za su rage matsalar rashin ingantaccen abinci a Jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here