Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za a dawo da jigilar jirgin ƙasan Abuja-Kaduna a ranar 5 ga Disamba.
Fidet Okhiria, Manajan Darakta na Kamfanin Jigilar Jirgin ƙasa na Najeriya, NRC ne ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, a jiya Alhamis, inda ya ce an shirya komai don ci gaba da ayyukan.
Okhiria, ya shawarci fasinjojin da ke son yin tafiye-tafiye a jirgin da su fara sabunta manhajar wayar hannu tun daga ranar 3 ga Disamba, don ba su damar yin yin tafiya.
A cewar shugaban NRC, ayyukan za a fara jigilar ne da jirage biyu daga Abuja zuwa Kaduna da kuma Kaduna zuwa Abuja.
“jirgin AK 1 zai tashi daga tashar Idu da karfe 9:45 na safe ya isa tashar Rigasa da karfe 11:53 na safe.
“AK 2 zai tashi daga Rigasa da karfe 8:00 na safe ya isa tashar Idu da karfe 10:17 na safe.
“AK 3 zai tashi daga tashar Idu da karfe 15:30 na safe ya isa tashar Rigasa da karfe 17:38 na safe.
” Kuma AK 4 zai tashi Rigasa da karfe 14:00 na safe su isa tashar Idu da karfe 16:07.
Shugaban na NRC ya tabbatar wa fasinjoji jajircewar Gwamnatin Tarayya na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a cikin jirgin a kowane lokaci.