Da yammacin ranar Laraba ne rikici ya barke tsakanin shugabannin jam’iyyar PDP na jihar Kano da wakilan hedikwatar jam’iyyar na kasa da zasu wakilci babban taron jam’iyyar a jihar.
Rikicin ya faru ne a Otal din Tahir inda daya daga cikin wakilan hedikwatar jam’iyyar ta kasa ya yada zango.
Rahotanni sun bayyana cewa bayan rikicin an mika wasu shugabannin jam’iyyar na jihar Kano, su biyu da suka hada da Dahiru Haruna da Idi Zare Rogo ga Ofishin ‘yan sanda dake Badawa.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Shehu Wada Sagagi ya shaidawa manema labarai cewa sun tarbi guda cikin wakilan jam’iyyar na kasa (mai suna Barista Ekwudile) a filin jirgin saman Malam Aminu Kano inda aka kai shi Otal Tahir, sai dai shi (Ekwudile) ya bukaci masu masaukin dasu kawo masa abin sha, suka fita domin a kawo masa.
“Lokacin da suka dawo dauke da abin shan kamar yadda ya bukata, ba su tarar da shi a cikin dakin ba amma daga baya sun gano shi a daki mai lamba 811 wadda anan ne rikici ya barke,” in ji shi.
Yace duk da yake bai da tabbas kan musabbabin rikicin, amma dai ana iya danganta shi da mutanen da suka ga Ekwudile tare da su, wanda a cewarsa watakila ya sa Dahiru Haruna da Idi Zare Rogo suka yi zargin cewa da akwai wata kullalliya.
Sai dai kuma jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tun a baya an samu baraka a jam’iyyar PDP ta Kano inda wasu ‘yan jam’iyyar ke biyayya ga tsohon ministan harkokin waje, Ambasada Aminu Wali kuma ke da nasu shugabancin amma shedikwatar Jam’iyyar ta Kasa Shehu Wada Sagagi ta amince da shi a matsayin shugaban Jam’iyyar na Jihar Kano.
Sagagi dai na daya daga cikin masu biyayya ga tsagin tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, wanda a baya bayan nan ya fice daga jam’iyyar ya koma Jam’iyyar NNPP.













































