Najeriya ba za ta halarci Gasar cin Kofin Duniya na 2026 da za a yi a Kanada, Amurka da Mesiko ba.
Wannan ya biyo bayan ta yi rashin nasara a fanareti da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a wasan neman gurbin shiga gasar ta Afrika.
An tashi wasan ne 1-1 bayan mintuna 90 da ƙarin lokaci, sai dai a bugun fanareti Kungiyar Leopards ta Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta samu nasara 4-3, abin da ya ba su gurbin shiga wasan share fage na nahiyoyi da za a yi a watan Maris shekara mai zuwa.
Najeriya ce ta fara cin kwallo da wuri a wasan na ƙarshe da aka buga a Rabat, Maroko, inda ɗan wasan tsakiya Frank Onyeka ya zura ƙwallo a farkon wasan ya ba Super Eagles damar jagoranci.
Super Eagles sun yi ƙoƙarin ƙara ƙwallo ta biyu amma suka kasa cinye damar da suka samu, lamarin da ya bai wa ‘yan wasan Kongo damar shiga cikin wasan sosai suna ɗaukar ragamar bugun wasa.
Mechak Elia ya dawo da kwallon daidai a minti na 32, inda hakan ya sa wasan ya tashi ɗaya-ɗaya har zuwa ƙarshen rabin farko, sannan kuma an ga cewa Victor Osimhen bai dawo filin wasa ba a zagaye na biyu.
Najeriya ta saka Akor Adams, wanda ke buga wasa a Sevilla, daga baya kuma Tolu Arokodare, Chidera Ejuke da Simon Moses, amma hakan bai kawo wani tasiri ba domin Super Eagles sun fi komawa baya yayin da Kungiyar Leopards ke ƙoƙarin samun nasara.
An tashi wasan har zuwa ƙarin lokaci inda Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta zura kwallo wadda aka soke saboda an yi wa Stanley Nwabali kuskure, sannan daga baya Nwabali ya yi babban tsayawa a ƙarin lokaci ya hana su cin kwallo a mintuna na ƙarshe, kafin a tafi bugun fanareti da suka yi nasara.













































