Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta sanar da neman dakataccen kwamandan jami’an leken asiri na rundunar ‘yan sandan Najeriya DCP Abba Kyari ruwa a jallo bisa zargin sa da hannu a cinikin Cocaine na kilogiram 25.
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta bayyana Kyari a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo a wani taron manema labarai da Daraktanta na yada labarai Femi Babafemi ya yi, a hedikwatar ta da ke Abuja a ranar Litinin 14 ga Fabrairu, 2022.
Hukumar ta ce ta dauki matakin ne bayan duk kokarin da aka yi na ganin ya amsa gayyatar hukumar domin amsa tambayoyi ya ci tura.
Hukumar ta koka kan yadda mutanen da ya kamata ace suna goyon bayan kokarin da ake yi na dakile matsalar fataucin miyagun kwayoyi amma sune suke taimakawa wajen aikata lefin.
Hukumar ta yi Karin haske kan wani binciken da ta gudanar kan cinikin magunguna. Labarin ya fara ne a ranar Juma’a 21 ga watan Junairu, 2022, lokacin da DCP Kyari ya kaddamar da kira ga daya daga cikin jami’an NDLEA a Abuja da karfe 2:12 na rana. Da jami’in ya mayar da kiran bayan mintuna biyu, sai Kyari ya sanar da shi cewa zai zo ya same shi, domin tattauna wani al’amari na aiki bayan kammala Sallar Juma’a.













































