Gwarzon musabaƙar Najeriya ya kuɓuta daga masu garkuwa da shi

8b6bd42c fff6 4688 8147 79cfb3707010.jpg

Iyalan mahaddacin Alkur’anin nan da ƴanbindiga suka sace a jihar Katsina tare da mahaifinsa sun ce sun kuɓuta daga hannun masu garkuwa da su.

Kimanin mako biyu da suka wuce ne dai aka sace Alaramma Abdulsalam Rabi’u Faskari, wanda ya zama gwarzon gasar karatun Alƙur’ani mai girma ta ƙasa da aka yi a jihar Kebbi tare da mahaifinsa da ƴanuwansa bayan gwamna jiharsa ta Katsina ya karrama shi.

Malam Rabiu Zakariya Faskari, shi ne mahaifinsa da aka sace su tare a yankin Faskari, ya bayyana wa BBC cewa sun tsira ne ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

Labari mai alaƙa: Zakaran gasar karatun Al-Qur’ani da aka sace shi da mahaifinsa da ‘yan uwansa har yanzu suna raye – Mahukunta

Ya ce asali a Katsina ne ƴanbindiga suke riƙe da su, sai ƙasurgumin ɗanbindiga, Yellow ya zo daga Zamfara, ya “ƙwace mu da ƙarfin tsaiya daga inda muke. Sai da ya musu dukan tsiya kafin ya tafi da mu,” in ji shi.

Ya ce an yi ciniki, amma ɗanbindigar ya ƙi amicewa. “Haka muka cigaba da zama muna addu’a, sannan ana yi mana addu’a. Sai ranar Juma’a kawai aka zo aka ce mana mu fito mu tafi. Yaransa suka ɗauko mu suka tsallako da mu dajin Munhaye suka kawo wani gari suka ajiye mu. Daga garin sai da muka yi tafiya ta awa huɗu.”

Ya ce da suka hau babur ne shi ne ɗan acaɓa ke faɗa musu an kashe shugaban dabar mai suna Yellow, “ashe shi ya sa yaransa suka sake mu muka tafi.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here