Gwamnatin tarayya ta sanar da ɗage jana’izar Aminu Dantata a Madina

Alhaji Aminu Alhassan Dantata

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana’izar fitaccen ɗankasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata daga yau Litinin zuwa gobe Talata.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a Mohammed Idris ya tabbatar wa da BBC ɗage jana’izar sakamakon rashin isar gawar marigayin a kan lokaci zuwa birnin Madina.

Ministan ya ce Akwai ƙa’idoji da gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa kan yadda za a shigar da gawa domin yi mata jana’iza a ƙasar, da ake ci gaba daa cike-ciken takardu tsakanin gwamnatin Saudiyya da iyalan mamacin.

Mohammed Idris ya ce idan an kammala za a ɗauko gawar daga Hadaɗɗiyar Daular Larabawa zuwa Saudiyya, da ya ƙara da cewar tuni ofishin jakadancin Najeriya a Saudiyya da iyalan mamacin suka kammala shirye-shiryen jana’izar.

Tun da safiyar yau Litinin ne tawagogin gwamnatin tarayya da na gwamnatin jihar Kano suka tafi Saudiyyar da nufin halartar jana’izar da aka shiryi yi a yau Litinin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here