Gwamnatin jihar Kano, ta haramta wa direbobin baburan Adaidaita Sahu bin manyan Titinan jihar.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA Nabilusu Abubakar Kofar Nai’sa ya fitar a daren jiya Litinin.
Sanarwar ta ta ce, Gwamnatin jihar Kano ta hannun Hukumar kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa KAROTA ta haramta wa matuƙa Baburin Adaidaita Sahu min manyan titinan daga gobe Laraba 30 ga watan Nuwamba, 2022.
Gwamnatin ta ɗauki matakin ne bayan da ta samar da manyan motocin da za su dinga ɗaukar al’umma a titinan da aka haramtawa yan Adaidaita Sahun.
Haka kuma, Sanarwar ta bayyana cewa an haramta wa direbobin baburan Adaidaita Sahun bin titinan Amadu Bello zuwa titin Munduɓawa zuwa Gazawa da titin Tal’udu zuwa Gwarzo.
Gwamnatin ta bayyana cewa ta tanadi manyan motocin sufuri domin sauƙaƙawa al’umma bin waɗannan hanyoyi.
Sanarwar ta ƙara da cewa, Gwamnatin jihar Kano za ta sanar da ranar da direbobin Adaidaita Sahun za su daina bin wasu manyan titinan da zarar ta samar da ababen hawan da al’umma za su yi amfani da su a waɗannan hanyoyi.













































