Gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq ya zama sabon shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF).
Abdulrazaq ya maye gurbin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal wanda wa’adin sa zai cika a ranar 29 ga watan Mayu.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Tambuwal ya sanyawa hannu a karshen taron gaggawa na gwamnonin jihohin kasar karo na 7 da suka gudanar a daren ranar Talata a Abuja.
Sanarwar ta ce an ayyana Abdulrazaq ne ta hanyar fahimtar juna yayin da aka zabi gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde a matsayin mataimakin shugaban kungiyar.
Sanatrwar ta ce “Mambobin kungiyar sun bayyana gamsuwarsu da nasarar da aka samu na nadin sabbin gwamnoni da masu dawowa daga ranar 14 zuwa 19 ga Mayu, 2023.
“Mambobin sun himmatu wajen ci gaba da yin hadin gwiwa a tsakanin jihohi ta hanyar inganta takwarorinsu, koyo a matakin kananan hukumomi da zurfafa dangantaka da gwamnatin tarayya da sauran cibiyoyi.
“A karshe shugaban kungiyar ya sanar da mambobin kungiyar cewa Ministar Kudi ta amince da bukatar kungiyar na gaggauta dakatar da ci gaba da cire kudi daga asusun jihohi don biyan bukatun kananan hukumomi wadanda suke na Paris Club, kuma kudaden da aka cire zuwa yanzu za a mayar da su ga jihohi.”













































