Gobara ta ƙone sassan Fadar Sarkin Jama’a a Kafanchan

Fire outbreak

Wata gobara da ta tashi a ranar Juma’a ta ƙone wasu sassa na Fadar Sarkin Jama’a da ke Kafanchan, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Jema’a a Jihar Kaduna.

Majiyoyi sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa NAN cewa ɗakunan da gobarar ta shafa na ɓangaren da mahaifiyar Sarkin ke zaune ne.

A cewar majiyoyin, gobarar ta tashi ne yayin da iyalan ke shirye-shiryen sallar Magariba, lamarin da ya haifar da firgici a cikin fada da ma unguwannin da ke kewaye.

Lokacin da NAN ta kai ziyara fadar a daren Juma’a, ta gano cewa har zuwa lokaci mai tsawo ana ganin hayaƙi da alamun ɓarnar da gobarar ta yi, inda wasu sassan ginin suka ƙone ƙurmus tare da lalata kayan gida da dama.

Shaidun gani da ido sun ce jami’an kashe gobara sun amsa kiran gaggawa, amma ba su samu nasarar shawo kan gobarar da wuri ba, domin na’urar famfon ruwansu ta ƙi aiki da isowarsu wurin.

Hakan ya kawo tsaiko a matakin farko na kashe gobarar, wanda ya ba ta damar yaɗuwa tare da cinye bangarori huɗu kafin a samu ƙarin taimako.

Wasu mazauna yankin sun haɗa kai domin ceto kadarori da kuma hana gobarar yaɗuwa zuwa sauran sassan fadar.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu asarar rai ba, sai dai gobarar ta janyo mummunar ɓarna.

Har yanzu ba a gano musabbabin gobarar ba, kuma hukumomi ba su fitar da cikakken bayani kan girman asarar ko yanayin faruwar lamarin ba.

Mazauna Kafanchan sun bayyana gobarar a matsayin abin takaici, tare da kira da a inganta ƙarfin martanin gaggawa a yankin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here