Gidauniyar Ganduje ta fara daukar ma’aikata a sabuwar kungiyar Hisbah mai zaman kanta a Kano

WhatsApp Image 2025 12 07 at 3.38.12 PM 750x536 1 750x430

Sabuwar kungiyar Hisbah mai zaman kanta ƙarƙashin gidauniyar Ganduje da ya samar,  ta fara raba fom din daukar ma’aika domin shiga aikin da take shirya aiwatarwa a jihar Kano.

Aikin kafa kungiyar na karkashin gidauniyar Ganduje.

Shirin kaddamar da fom din shiga aikin an gudanar da shi ranar asabar a Kano, karkashin Babban Daraktan Cibiyar samar da kayayyaki ta kasa kuma jigo a jam’iyyar APC, Hon. Baffa Babba Dan Agundi, tare da tsohon kwamandan Hisbah na jihar Kano, Sheikh Haruna Ibn Sina.

Kungiyar ta bayyana cewa wannan shiri na kungiyar Hisbah mai zaman kanta “Independent Hisbah Fisabilillah” ba hukumar gwamnati ba ce, domin an kafa ta ne a matsayin ƙungiyar sa-kai da ke yin ayyukan addini da na jin ƙai.

Karin labari: Kafa sabuwar hukumar Hisba mai zaman kanta da Ganduje ke niyya ba ta dace da kundin tsarin mulki ba, kuma barazana ce ga zaman lafiyar jiha – Lauya

Ibn sina ya bayyana cewa ƙirƙirar wannan Hisbah mai zaman kanta na da nufin samar da sabon dandalin aikin yi ga mutane 12,000 da aka dakatar daga aikin hisbah na gwamnati, domin su sami damar ci gaba da hidimtawa al’umma.

A cewarsa, kafa wannan sabuwar hisbah an yi ne domin gudanar da ayyuka na tsaro ta fuskar addini, da kuma tallafa wa al’umma ba tare da rage matsayin hukumar Hisbah ta gwamanti ba.

Gidauniyar ta Ganduje na ci gaba da karɓar buƙatu daga duk wanda ke son shiga wannan shiri, tare da bayyana cewa za a gudanar da horaswa ga duk wadanda suka samu nasarar shiga aikin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here