Gidauniyar Al-Mubarak Waqf, ta raba Naira miliyan biyu da dubu ɗari tara ga mutane goma sha ɗaya da makarantar Ubayy Ibn Ka’ab Academy, da kuma Gidauniyar Tallafawa marayu.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa shugaban hukumar gidan rediyon Freedom, Alhaji Ado Muhammad, shi ne ya raba cakin kuɗin ga wadanda suka amfana a shalkwatar gidauniyar da ke Kano.
Alhaji Ado Muhammad ya ce gidauniyar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen samar da irin waɗannan abubuwan ga mabukata.
Ya kuma shawarci masu hannu da shuni kan buƙatar bayar da isasshiyar Zakka da nufin zama jari ga masu cin gajiyarta.
A cikin wata ƙasida da ya gabatar mai taken ‘Preamble Al-Mubarak Waqf Foundation’ mamba a kwamitin amintattu na gidauniyar, Dakta Jamilu Chedi ya ce, gidauniyar ta fi bada fifiko ga ilimi da bunkasa jarin ɗan Adam.
A cewarsa an kafa gidauniyar ne a shekarar 2019, da nufin taimakon al’ummar musulmi.
Ya ce tallafawa harkokin ilimi da kasuwanci da fasaha ga al’ummar musulmi na daga cikin manyan manufofin gidauniyar.
Shi ma da yake jawabi, shugaban kwamitin gudanarwa na gidauniyar Malam Saleh Adamu Kwaru ya bayyana cewa gidauniyar na gina masallacin Juma’a da cibiyar fasahar sadarwa a unguwar Na’ibawa.
Da yake jawabi a madadin waɗanda suka ci gajiyar shirin, Junaidu Ahmad ya gode wa gidauniyar bisa irin karamcin da ta musu tare da yin alkawarin yin amfani da zakkar da ta basu yadda ya dace.













































